Tabarbarewar tsaro a Nigeria na shafar abinci a Niger

noma a Niger Hakkin mallakar hoto b
Image caption noma a Niger

A jamhuriyar Nijar, wasu al'umomin yankin Cintabaraden a arewacin jahar Tawa na ci gaba da kokawa dangane da mayuwacin halin da suka shiga sakamakon matsalar tabarbarewar tsaro da ta addabi wasu sassan Najeriya.

Kazalika, al'ummomin yankin na kokawa da jami'an kwastan da suka ce na kawo cikas ga shigo da kayayyakin abinci daga kasar Aljeriya mai iyaka da Nijar din, abin da ya sa farashin kayayyakin abincin ya yi tashin gwauron zabo.

A yanzu haka buhun gero ya kai jika 25 na CFA yayin da farashin dabbobi da su ne mazauna yankin ke dogaro da su ya fadi.

Karin bayani