An yi zaben gwamna a Adamawa lafiya

Masu zabe a Najeria Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Masu zabe a Najeria

Rahotanni daga jihar Adamawa a nijeriya na cewa an fara tattara sakamakon zaben gwamnan jihar da aka gudanar a yau cikin tsauraran matakan tsaro.

Kodayake bayanai daga wasu wurare na cewa mutane da dama sun fito domin jefa kuri'ar, amma a wasu yankunan jama'a baasu fito sosai ba.

An dai kammala kada kuri'a lami lafiya inda kuma jam'iyyu biyar suka shiga zaben, wadanda suka hada da ACN da ADC, da ANPP da CPC, da kuma jam'iyyar PDP mai mulki.

Karin bayani