An gudanar da zanga zanga a Moscow

Masu zanga zanga a Moscow Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga zanga a Moscow

Dubban masu zanga zangar nuna adawa da Praministan Rasha, Vladimir Putin, sun yi maci a birnin Moscow, duk kwa da tsananin sanyin da ake.

Sun yi kiran da a yi sauye sauyen siyasa, sannan a sake gudanar da zaben 'yan majalisar dokokin kasar na watan Disamba, wanda suka ce an tafka magudi a lokacinsa.

Masu zanga zangar sun yi kira ga jama'a da kada su zabi Vladimir Putin, a zaben shugaban kasar na watan gobe.

Magoya bayan mista Putin din sun gudanar da kishiyar zanga zanga a wani wurin na dabam.

Karin bayani