Majalisar dinkin duniya za ta kada kuria kan Syria

Kwamitin sulhu game da Syria Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kwamitin sulhu game da Syria

Jamian diflomasiyya a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya sun ce za su kada kuria a yau na goyon bayan matakin da kungiyar hadin kan larabawa ta dauka kan Syria.

Kasashen turai da na Larabawa ne suka dauki nauyin wannan kuduri.

To saidai babbar kawar Syria wato Russia ta bayyana adawar ta da wasu sassan kudurin, kuma babu tabbaci ko za ta yi amfani da huruminta na hawa kujerar na ki don adawa da kudurin.

Banbance banbance game da Syria ya takaita aiyukan kwamitin sulhun na tsawon watanni.

Karin bayani