An gaza amincewa da kuduri kan kasar Syria

An gaza amincewa da kuduri kan kasar Syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rasha da China ne suka hau kujerar naki kan kudurin

Kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gaza amincewa da daftarin kudurin da kungiyar kasaashen Larabawa ta gabatar kan rikicin kasar Syria, wanda kuma ke samun goyon bayan kasashen Yamma.

Kasashen Rasha da China ne suka hau kujerar naki kan kudurin - wanda ya nemi shugaba Bashar Assad ya yi murabus.

Gwamnatocin kasashen Yamma sun soki matakin na Rasha da China.

Babu shakka matakin da kwamitin sulhun ya dauka ba zai yiwa masu fafutuka a kasar ta Syria da kuma shugabannin kungiyar kasashen Larabawa dadi ba, ganin cewa sun kwallafa rai domin ganin kwamitin sulhun ya yi wani abu.

'sakamakon watsi da shi'

Tuni dai dama kasar Rasha ta ce ba za ta goyi wannan kudurinba, kuma ta cika alkawarin na ta, inda harma ta samu goyon kasar China wacce ita ma ta yi watsi da kudurin, kamar yadda shugaban kwamitin sulhun wato Kodjo Menan daga kasar Togo ya bayyana ta hanyar tafinta:

"Ba a amince da wannan daftarin kuduri ba, sakamakon watsi da shi da kasashe biyu na kwamitin sulhun suka yi".

Matakin da Rasha da China suka dauka dai ba zai ba masu sharhi mamaki ba ganin cewa suna da alakar kut-da-kut da shugaba Bashar Assad.

Sai dai ya yi matukar batawa jami'an diflomasiyyar kasashen Yamma rai, inda jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice, ta ce a yanzu mutanen Syria sun san wadanda ke marawa yunkurinsu na samun 'yancin siyasa da fadar albarkacin baki baya, da kuma wadanda ba sa goyon bayan hakan.

Sai dai anasa bangaren jakadan Rasha a MDD Vitaly Churkin ya dora alhakin gazawar kudurin ne kan mambobuin kwamitin da ya ce sun sanya wata manufa ta daban a cikin lamarin.

Ya kara da cewa rasha ta yi koarin ganin an samu kuduri na gaske wanda zai taimaka wajen samar da zaman lafiya da kuma ci gaban siyasa a Syria.

Yayin da ake ci da gaba dambarwar diflomasiyya a Majalisar Dinkin Duniya, can a birnin Homs kuwa jimamin mutane sama da dari biyu ake yi, wadanda masu fafutuka suka ce dakarun Syria sun kashe a farmaki da suka kaddamar a birnin.

Mazauna birnin sun bayyana cewa an kai wani gagarumin hari a yankin Khaldiyeh.

Sai dai kuma ba wata kafa da ta tabbatar da yawan mutanan da harin ya ritsa da su, idan kuma har hakan ta tabbata to kuwa wannan zai kasance hari mafi muni da aka kai, tun bayan da aka fara rikicin na Syria watanni goma sha dayan da suka wuce.

Karin bayani