Murtala Nyako ya lashe zaben Adamawa

Murtala Nyako Hakkin mallakar hoto google
Image caption Kwanaki goma da suka wuce ne kotu ta sauke Murtala Nyako

Hukumar zabe a Najeriya INEC ta bayyana tsohon gwamnan jihar Adamawa Vice Admiral Murtala Nyako na jam'iyyar PDP mai mulkin kasar, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Mr Nyako ya samu nasara ne a kan abokin hamayyarsa na jam'iyyar Action Congress Markus Gundiri, wanda ya zo na biyu.

Dan takarar jam'iyyar CPC Birgadiya Janar Buba Marwa shi ne ya zo na uku, yayin da dan takarar jam'iyyar ANPP ya zo na hudu.

"Murtala Nyako ya cika dukkan sharadan da tsarin mulki da kuma dokar zabe ta tanada, a don haka shi ne zababben gwamnan jihar Adamawa," a cewar babban jami'in zaben Farfesa Mohammed H. Mohammed.

To sai dai kuma tuni wasu 'yan adawa a jihar suka yi fatali da sakamakon zaben wanda aka gudanar cikin tsauraran matakan tsaro.

Zaben na jihar Adamawa shi ne zaben gwamna na farko da aka yi a Najeriya tun bayan da kotun kolin kasar ta sauke gwamnoni biyar na wasu jihohi a kasar ciki harda na jihar ta Adamawa, saboda a cewar kotun suna kan karagar mulkin ne ba bisa ka'ida ba domin kuwa wa'adinsu ya kare tun a watan Mayun bara.