Rasha da China na shan suka akan Syria

Dakarun gwamnatin Suria a Homs Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Dakarun gwamnatin Suria a Homs

Matar nan 'yar kasar Yemen da ta sami kyautar Nobel ta zaman lafiya, Tawakul Karman, ta ce China da Rasha ne ke da alhakin kashe-kashen da ake a Syria, bayan da a jiya kasashen biyu suka hau kujerar na-ki a kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, dangane da wani kudurin da ya shafi Syriar.

Ta ce, Bashar al-Assad ya aikata wadannan munanan laifukan tare da goyon bayan Rasha da China, ba kunya ba tsoron Allah.

Tawakul Karman ta kuma goyi bayan kiran da Tunisia ta yi ga kasashen larabawa, na su bi sahunta, wajen korar jakadun kasar Syria.

Babbar kungiyar adawan Syria, SNC, ta yi Allah wadai da matsayin Rasha da Chinar, wanda ta ce ya ba gwamnatin Syriar izinin hallaka jama'a.

Amma kafofin yada labaran gwamnatin Syriar sun yabawa Rasha da Chinar ne.

Suka ce hawa kujerar-na-kin da suka yi, zai kara wa gwamnati karfin gwiwar cika alkawarin da ta yi, na yin sauye sauyen siyasa.

A Syriar, mayakan 'yan tawaye a Homs sun ce, sojojin gwamnati, tare da tankunan yaki da kuma bindigogin atilare, suna jan daga a kewayen babban yankin da ke karkashin ikon 'yan adawa.

A cewar wani wakilin BBC a Homs din, an shaida masa ana tono gawarwakin jama'a, daga karkashin dogayen gine-ginen da suka rushe a daren Juma'a, sakamakon hare-hare daga tankunan yaki da manyan bindigogi.

Gwamnatin Syria ta yi watsi da rahotannin da ke cewa, dakarunta sun kai mummunan hari a birnin na Homs.

Ta ce, karya ce kawai.

Karin bayani