Za a aurar da zawarawa 1000 a Kano don samar da tsaro

Matan aure Hakkin mallakar hoto bbc

Gwamnatin Jihar kano dake arewacin Nigeria ta ce za ta aurar da zawarawa Dubu daya a karon farko dan magance matsalar rashin tsaro a jihar.

Hukumar Hizba ce ta fito da tsarin, inda ta ce kuma bayan karo na farko da za'a yi za kuma a ci gaba, har sai an rage yawaitar matsalolin da ake fuskanta ta mace-macen aure.

Hukumar tace a wannan watan ne za ta fara tantance maza da mata masu san auren, inda da zarar an samu za'a yi gagarumin taro na daura aure a rana daya.

Kungiyar zawarawa da marayu dai ta yi maraba da wannan yunkuri.

A cewar Malam Aminu Ibrahim Daurawa wanda shi ne kwamandan hukumar Hizba ta jihar Kano da ta fito da tsarin, sun lura cewa rashin samun cikakkiyar kulawa daga iyaye na daga abubuwan da suke kara tabrbara al'amuran tsaro a jihar.

A cewar shugaban na Hizba, a kashin farko na wadanda za'a aurar harda shugabar kungiyar Zawarawan jihar Hajiya Atine Abdullahi, kuma yayin da wakilin BBC Yusuf Ibrahim Yakasai ya isa gidanta, ya tarar ana gyare-gyare da shara ta musamman wadda ta tabbatar da cewa duk suna da alaka da shirin auren.

Shugabar ta zawarawa da marayu tace ko da dai suna da zabin irin mazan da suke so, amma babban zabi sun barwa Allah ya yi musu zabi mafi alkhairi.

Karin bayani