'Yan bingida sun hallaka wani mutum a Damaturu

Hakkin mallakar hoto google
Image caption 'Yan sandan Najeriya

A Najeriya, wadansu mutane da ba 'a san ko su wanene ba, sun hallaka wani mutum da ake kyautata zaton jami'in tsaro ne a garin Damaturu na jihar Yobe da ke arewacin kasar.

Ganau sun ce mutanen sun zo ne a kasa, inda suka harbi mutumin mai suna Muhammad Umar Shattima, wanda ke tare da wasu mutanen, sannan suka ranta a na kare.

Rundunar 'yan sandan jihar dai ta tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai ta kara da cewa tana gudanar da bincike.

Jihar yobe dai na daga cikin jihohin da ke fuskantar hare-hare na kungiyar Jama'atu Ahlussunnah Lid- da'awati wal jihad wadda aka fi sani da suna Boko Haram.