An kai hari wani ofishin 'yan sanda a Kano

Boko Haram
Image caption Boko Haram ta sha kai hare-hare a Najeriya

Wasu 'yan bindiga sun kai hari kan wani ofishin 'yan sanda a birnin Kano da ke Arewa maso yammacin Najeriya.

Wadanda suka shaida lamarin sun shaida wa BBC cewa an ji karar harbe-harbe da fashe-fashen wasu abubuwa a unguwar Sharada da ke wajen birnin na Kano.

Rahotanni sun kuma ce ana yin musayar wuta tsakanin sojoji da wasu mutane a Unguwar Mariri.

Wata majiya a unguwar ta Mariri wacce ke kan titin Maiduguri, ta shaida wa BBC cewa jami'an sojin sun zagaye wani gida inda kuma ake ta yin musayar wuta da mutanen da ke cikin gidan.

An kuma ji karar fashewar wani abu a wata kasuwa a birnin Maiduguri da ke Arewa maso Gabashin kasar.

Wata mazauniyar birnin Maiduguri Aisha Goni ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP: "Na ji fashewar abubuwa biyar, kuma hayaki daga kasuwar ya turnuke sararin samaniya.

"Har yanzu kasuwar na cin wuta. Sojoji da 'yan sanda sun kewaye yankin."

A watan da ya gabata ne kungiyar Boko Haram ta kai wasu munanen hare-hare wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kusan 200.

Boko Haram na fafutukar kafa shari'ar Musulunci ne a wasu sassan Najeriya, sai dai 'yan kasar da dama basu gamsu da yadda kungiyar ke gudanar da al'amuranta ba.

Karin bayani