Amurkawa za su fuskanci tuhuma a Masar

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ma'aikatan kungiyoyin tabbatar da dimokaradiyya a Masar.

Amurka ta ce ta yi matukar damuwa da jin cewa fiye da mutane arba'in 'yan kungiyar da ke rajin kare mulkin Dimokaradiyya a kasar Masar ne za a tuhuma.

Gwamnatin kasar dai ta cafke mutanen ne bayan da ta zarge su da gudanar da ayyuka ba bisa ka'ida ba, da kuma karbar taimakon kudade daga kasashen waje don tayar-da-zaune tsaye a kasar.

Cikin mutanen har da Amurkawa goma sha tara wadanda suka hada da dan gidan sakataren sufuri na kasar, Ray LaHood.

Wannan lamari dai ya zo ne a sa'ilin da dangantaka ke ci gaba da yin tsami tsakanin Amurka da gwamnatin Masar.

Masar dai za ta yi asarar dala biliyan daya da rabin da take samu daga Amurka idan majalisar dokokin Amurkan bata gamsu da ayyukan da take gudanarwa na tabbatar da mulkin dimokaradiyya ba.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta nuna rashin jin dadinta game da abubuwan da ke faruwa a Masar din, tana mai cewa za ta bukaci karin bayani daga wajen gwamnatin kasar.