Ana neman karin abinci a Nijar

Noma a Nijar Hakkin mallakar hoto b
Image caption Noma a Nijar

Gwamnatin Nijar ta ce, gibin da aka samu ta fannin cimaka, sakamakon rashin kyaun damanar da ta gabata, ya wuce abin da gwamnatin ta yi hasashe tun farko.

Haka lamarin yake kuma ta bangaren abincin dabbobi.

Karancin abincin ya shafi kusan dukan jahohin kasar, ko da yake matsalar ta fi kamari a jahar Diffa.

A baya dai gwamnati ta ce ana bukatar fiye da ton dubu 500 ne.

To amma yanzu abinda ake bukatar ya kusan ton 700.

Gwamnati ta ce, ta dau matakan da suka hada da soma shirin nan na sayar da cimaka a cikin farashi mai rahusa.

Karin bayani