Sarauniyar Ingila ta cika shekaru 60 a gadon sarauta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sarauniyar Ingila, Elizabeth

A ranar Litinin ce ake bikin cika shekaru sitti da hawan sarauniya Elizabeth ta Ingila gadon sarauta.

A wani sako da ta aike, sarauniyar ta bayyana godiyarta ga wadanda suka bata goyon baya da kuma karfafa mata gwiwa a shekaru sittin din da ta shafe akan gadon sarauta.

An dai shirya wasu taruka a wannan rana don gudanar da jawabai game da sarauniyar Ingilar.

Sarauniya Elizabeth ta soma mulki ne bayan da mahaifinta Sarki George na shida ya rasu a ranar shida ga watan Fabrairu ta shekarar 1952.

Wannan wata rana ce ta murna ga sarauniyar da kuma tunawa da abubuwan da suka faru a baya.