Mu muka kai hare-haren Kaduna - Boko Haram

hare-haren Kano Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Boko Haram ta kuma kai wani harin a birnin Kano ranar Litinin

Kungiyar Boko Haram ta ce ita ce ta kai hare-haren bama-baman da suka tashi a garin Kaduna na Arewacin Najeriya, da kuma wanda aka kai a Kano ranar Litinin.

An kai hare-haren na Kaduna ne - wanda cikinsu nar da na kunar bakin wake ga barikin sojoji na Dibijin na Daya ko kuma One division da ke Unguwar Kawo.

Haka nan kuma rahotannin sun ce wani bomb din da aka dana a karkashin gadar Kawo, ya yi kaca-kaca da wasu motoci guda hudu.

Tuni dai Sojoji suka killace barikin na One Division, inda kuma rahotanni suka nuna cewar da dama sun jikkata a wannan hari.

Baya ga wadannan hare-hare, an kuma ce wani bomb din shi ma ya fashe a sansanin mayakan sama da ke unguwar Mando a Kadunar.

Mai magana da yawun Hukumar bada agaji na gaggawa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutane da dama sun samu rauni sanadiyyar tashin bama-baman.

A nata bangaren rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da harin, inda ta ce dan kunar bakin-wake ne ya kai harin, amma shi kadai ne ya rasa ransa.

Sai dai tuni ta dora alhakinsa kan Kungiyar jama'atu Ahlissunnah Lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram.

Daukar alhaki

Wani da ke ikirarin magana da yawun kungiyar Boko Haram da ya kira kansa da lakabin Abu Qaqa, ya ce "gwamnatin Najeriya ba abar a amince da ita ba ce, domin sun baiwa gwamnati damar tattaunawa kamar yadda ta bukata, ta hanayar kyale mai magana da yawunsu ya fito, amma gwamnatin ta kame shi.

Don haka suka kai hari Kaduna, kuma za su ci gaba da kai hari duk wani gari da aka tona asirin 'yan kungiyar ko kuma aka kama musu mambobi".

'Yan kungiyar ta Boko Haram sun kira manema labarai a Maiduguri ta wayar tarho inda suka yi wannan ikirari, kuma wasu daga cikin 'yan jaridun da suka tattauna da 'yan Boko Haram din sun tabbatar wa da BBC cewa kungiyar ta tuntube su ne ta hanayar da ta saba tuntubar 'yan jaridu.

Kungiyar ta kuma karyara ikirarin da wasu matasa biyu suka yi a gidan talabijin na kasar cewa kungiyar ta kafa 'yan kwamiti da za su tattauna da gwamnati wadanda suka kunshi Dr Shettima Ali Munguno, da tsohon gwamnan jihar Yobe Bukar Abba Ibrahim da kuma Malama Aisha Wakil.

"Mutumin da jami'an tsaro suka kama sunan sa Abu Darda, amma ya ari sunan Abu Darda a lokuta da dama wajen magana da 'yan jaridu a matsayin Abu Qaqa, don haka idan jami'an tsaro sun ce Abu Qaqa suka kama ba abin mamaki bane in ji shi.

Dangane da mutane bakwai da aka yanka kwanakin baya a Maiduguri kuwa, mai magana da yawun kungiyar ya ce wadanda aka yanka ba mabobin kungiyar su bane, face mutanen da suka hada baki da su wajen tona asirin 'yan kungiyar su goma sha daya da aka kashe a baya.

'dakarun sojin sun yi hanzari'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kungiyar ta dade tana kai jami'an tsaro da ma farar hula hari

Kungiyar ta kuma ce ba daidai bane ikirarin da iyayen mutane goma sha dayan suka yi na cewa ba 'yan kungiyar ba ne, domin in ji mai ikirarin magana da yawun kungiyar, "Boko Haram ta jima tana wa'azi a Maiduguri har tsawon shekaru takwas, don haka sun samu magoya baya wadanda wasu ba lallai suna yi wa kungiyar aikin kisa bane, ana basu wasu ayyukan na daban ne.

Kungiyar ta kuma karyata cewa ta yi kira ga Kiristoci da su bar arewacin Najeriya, Musulmi kuma su bar kudancin Najeriya".

Rundunar sojojin ta ce maharin dan kunar-bakin-wake ne sanye da kayan damara irin na sojoji, wanda ya jibge motar da yake ciki da boma-bomai kana ya tukata zuwa kofar barikin, inda ya nemi shiga da karfin tsiya.

Kakakin rundunar Manjo-janar Rafel Isa ya shaida wa BBC cewa dakarun sojin sun yi hanzari wurin hana maharin kaiwa ga gaci.

Ya kara da cewa maharin ya rasa ransa nan-take, kuma illar da boma-boman da suka tarwatse suka yi ga wasu gine-gine a barikin, sai dai babu wasu da suka jikkata.

Sai dai yayin da rundunar sojojin Najeriyar ke ikirarin cewa jami'anta sun harbe maharin tun a mashiga, binciken da BBC ta yi ya tabbatar da cewa maharin ya samu shigewa wasu daga cikin kofofin kafin kafin a bindige shi.

Karin bayani