An tuhumi jami'an gwamnatin Ghana

Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Shugaba John Atta Mills na Ghana

An tuhumi wasu manyan jami'an gwamnatin kasar Ghana su hudu da laifin karbar rashawa.

Ana zargin wani dan kasuwa kuma mai goyon bayan jam'iyyar NDP mai mulki, Alfred Agbesi, da laifin sace miliyoyin daloli daga bautul malin kasar.

Ana kuma tuhumar babban lauyan wata Jaha tare da matarsa, da kuma wani daraktan ministan kudin kasar, Paul Asimenu, da laifin taimakawa wajen aikata laifin.

Dukkanin mutanen hudu dai sun ki amsa tuhume-tuhumen da ake yi musu.

Masu aiko da rahotanni sun ce shari'ar na zuwa ne bayan da aka tilastawa wadansu manyan ministoci biyu sauka daga kan kujerarsu a watan jiya.