Hare-haren bam a jihar Kadunan Najeriya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Rahotanni daga Kaduna, sun ce an kai wasu hare-hare, da suka hada da harin da ake kyautata zaton na kunar bakin wake ne ga barikin sojoji na Dibijin na Daya ko kuma One division da ke Unguwar Kawo a Kadunar.

Haka nan kuma rahotannin sun ce wani bomb din da aka dana a karkashin gadar Kawo, ya yi kaca-kaca da wasu motoci guda hudu.

Tuni dai Sojoji suka killace barikin na One Division, inda kuma rahotanni ke nuna cewar akwai wadanda suka jikkata a wannan hari.

Baya ga wadannan hare hare, an kuma ce wani bomb din shi ma ya fashe a sansanin mayakan sama da ke unguwar Mando a Kadunar.

Mai magana da yawun Hukumar bada agaji na gaggawa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutane da dama sun samu rauni sanadiyar tashin bama-baman.

Yanzu zuwa yanzu dai ba a tabbatar da ko an rasa rai ba.

Amma ya zuwa yanzu jami'an tsaro sin killace wuraren da abun ya faru.

Ya zuwa yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kaddamar da harin. Najeriya dai na fama da matsaoli tsaron wanda su ka danganci kai hare-hare bama-bamai wanda kungiyar Boko Haram ta ke daukar nauyin kaddamarwa.