Mutane na kauracewa gidajensu a Kano

Boko Haram
Image caption Boko Haram ta kashe mutane kusan 200 kwanakin baya a Kano

Wasu mazauna yankin Gado a unguwar Mariri ta birnin Kanon Najeriya na kauracewa gidajensu tun bayan da aka shafe sa'o'i ana musayar wuta a unguwar a daren Talata.

Mazauna unguwar sun ce suna barin gidajen na su ne saboda tsoron kada abin da ya faru a daren Talatar ya sake faruwa, abin da suka ce ya tayar musu da hankali.

Mazauna unguwar dai na zaune cikin fargaba sakamakon sa'o'i da aka shafe ana musayar wuta tsakanin sojoji da wasu 'yan bindiga a wani gida.

Rahotanni daga yankin sunce tun misalin karfe biyar na yammacin ranar Litinin ake musayar wuta inda kuma aka wuce karfe goma sha biyun daren ba'a daina ba.

Wasu daga mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa basu yi bacci ba, saboda fargici da tsoron rashin sanin mai zai faru da su.

Wakilin BBC a Kano Yusuf Yakasai wanda ya ziyarci unguwar ta Gado a Mariri dai ya mazauna wurin sun shaida masa cewa "sojoji da dama ne suka yiwa unguwar tsinke bayan da suka bi wani mutum inda ya shige wani gida".

Lamarin dai yasa wasu daga mutanen unguwar tare da iyalensu sun kauracewa gidajensu, yayin da wasu kuma suka kwana cikin fargaba da tashin hankali.

Wasu kuwa sun yi kira ne ga mahukuntan kasar da su dauki matakai domin a samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar.

Harin da jami'an tsaron suka kai unguwar ta Mariri dai na zuwa ne a daidai lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hari ofishin 'yan sanda na Sharada, inda suka jefa wani abin fashewa da ya kona ofishin kamar yadda wata majiyar 'yan sanda ta shaida wa BBC tare kuma da raunata akalla dan sanda daya.

Kafin hare-haren na jiya dai kwanaki Tara aka yi cir ba'a samu wani tashin hankali a Kanon ba, tuna bayan hare-haren bama-bamai da aka kai a jihar, abinda ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 200.

Karin bayani