Terry ba zai bar tawagar Ingila ba

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption John Terry har wa yau na rike mukamin kyaftin a kungiyar Chelsea

BBC ta samu rahotannin dake nuni da cewa John Terry baya tunanin yin murabas daga tawagar kwallon Ingila.

Hukumar kwallon Ingila dai ta tsige Terry ne a matsayin shi na kyaftin din Ingila a ranar juma'ar da ta gabata.

Terry zai tsaya gaban shari'a ne a watan Yuli, game da zargin kalamun wariyar launin fata da ya yiwa dan wasan QPR, Anton Ferdinand.

Wata majiya da ke kusanci da Terry ta shaidawa BBC cewa, dan wasan baya tunanin daina takawa kasarsa leda.

Kocin Ingila dai Fabio Capello ya nuna rashin dadinsa da matakin da Hukumar ta FA ta dauka a kan Terry.

Wannan ne dai karo na biyu da ake tsige Terry daga mukamin na kyaftin.