Argentina ta zargi Burtaniya da yunkurin mamaye Falkslands

Hakkin mallakar hoto reuters
Image caption Cristina Fernan-dez de Kirchner

Shugabar Argentina, Cristina Fernan-dez de Kirchner, ta ce kasar ta za ta gabatar da koke ga Majalisar Dinkin Duniya dangane da wani mataki da Burtaniya ta dauka na tura daya daga cikin jiragen yakin ta na zamani zuwa tsibirin Falklands.

A yayin da take jawabi ga 'yan siyasa da wasu tsofaffin 'yan mazan-jiya, Mrs Kirchner ta zargi Burtaniya da kokarin mayar da yankin Kudancin tekun Altantika wani waje da take gudanar da harkokin sojin ta.

Shugabar ta ce gudanar da harkokin sojin da Burtaniya ke yi a wannan yanki na matukar barazana ga tsaron kasashen duniya.

Ta ce ta baiwa Sakataren Harkokin Wajen kasar umarnin gabatar da wannan koke a hukumance ga kwamatin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, da ma babban zaure na Majalisar don daukar mataki.

Ita dai Burtaniya ta ce ta kai jiragen yakin ta zuwa yankin ne kamar yadda ta saba, sai dai a kasar Argentina, mutane ba su gamsu da wannan bayani ba.

Karin bayani