Shugaban Sudan zai kaddamar da hukumar kula da Darfur

Shugaba Omar Al -Bashir na Sudan Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana shirin kaddamar da hukumar kula da yankin Darfur

A ranar Laraba ne Shugaba Omar al-Bashir na kasar Sudan zai kaddamar da hukumar kula da yankin Darfur.

Hukumar za ta rinka sa ido ga aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya ga lardin Darfur da ke yammacin kasar.

Yarjejeniyar wadda aka kulla a birin Doha na Qatar a bara, ta yi tanadin rabon ikon mulki, da arziki, da biyan diyya ga wadanda yaki ya shafa da komawar wadanda yakin ya kora daga gidajen su, da yin adalci da kuma tabbatar da tsaro.

Kungiya daya ce kadai ta rattaba hannu kan yarjejeniyar, yayin da sauran uku suka ki amincewa da ita.

Karin bayani