Wasu na ficewa daga kauyuka a Nijar don kaucewa yunwa.

A Jamhuriyar Nijar, yanzu haka mutane da dama ne ke ficewa daga daga kauyuka a jahar Tillaberi wadda aka ambato a sahun gaba wajen matsalar karancin abinci a wannan shekara.

Galibin wadanda ke ficewar dai na shiga birane kamar su Yamai ne don neman abinci.

Rahotanni dai sun nuna cewa akasarin mutanen dake ficewar matane ne da yaransu. Nijar dai na daga cikin kasashen da hukumar tarayyar Turai ta ce zata taimakawa a yankin Sahel, a Afirka kudu da Sahara, wadanda aka yi hasashen zasu fuskanci matsalar yunwa.

Gwanatin Nijar ta fara saida kayan abinci akan farashi mai rahusa don rage kaifin matsalar