An kaddamar da babban kamfanin siminti a Najeriya

Aliko Dangote
Image caption Aliko Dangote

A Najeria an kaddamar da kamfanin simintin da aka ce shi ne mafi girma a yankin Afirka na kudu da hamadar Sahara, a garin Ibase na jahar Ogun.

Ana sa ran kamfanin, wanda mallakar hamshakin mai kudin nan ne, Alhaji Aliko Dangote, zai taimaka wajen rage matsalar karanci da tsadar simintin da ake fuskanta a Najeriya, da ma wasu kasashen Afirka.

Za a kuma samu ayyukan yi kimanin dubu goma.

Manyan jami'ai daga ciki da kuma wajen Najeriyar ne suka halarci bikin kaddamarwar, ciki har da shugaba Goodluck Jonathan.

Karin bayani