BBC navigation

Najeriya na fuskantar rugujewa, in ji shugaban cocin Ingila

An sabunta: 9 ga Fabrairu, 2012 - An wallafa a 06:01 GMT
Shugaban cocin Ingila Dr. Rowan Williams

Shugaban cocin Ingila Dr. Rowan Williams ya ce Najeriya na fuskantar barazanar rugujewa

Archbishop na cocin Canterbury ta Ingila Dr. Rowan Williams ya yi gargadin cewa Najeriya na fuskantar barazanar rugujewa a hannun 'yan kungiyar jama'atu ahlussunna lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram .

Shugaban cocin Ingila din ya kuma bukaci gwamnatin Burtaniya ta taimakawa Najeriya don kare mabiya wasu addinnan.

Kalaman na shugaban cocin sun yi dai dai da na tsohon jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell, wanda shi ma ya yi hasashen rabewar kasar.

Masu sharhin al'amuran yau da kullum a Najeriya dai na ganin cewa matsalar da ke fuskantar kasar bata wargajewa ba ce, matsala ce ta rashin shugabanci mai nagarta.

Ita dai gwamnatin Najeriya ta sha bayyana cewa kasar tana nan a dunkule kuma babu abin da zai raba ta.

Kari a kan wannan labari

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.