Nijar ta yi Allah-wadai da kalaman Saadi

Shugaba Mahamadou Issoufou Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Mahamadou Issoufou na Nijar

Kakakin gwamnatin Jamhuriyar Nijar, Malam Marou Amadou, ya ce kasarsa ba za ta amince wani mutum ko wadansu mutane su yi amfani da ita ba domin kai hari a kan wata kasa.

Malam Marou Amadou ya fadi hakan ne yayin wani taron manema labarai da ya kira, inda ya yi tsokaci a kan kalaman dan tsohon shugaban kasar Libya, Saadi Gaddafi.

Shi dai Saadi ya shaidawa gidan talabijin na Al-Arabia cewa yana shirye-shiryen mayarwa sababbin mahukuntan kasar ta Libya, NTC, da martani daga Nijar din, inda yake gudun hijira tun watan Agustan da ya gabata.

Saadi Gaddafi ya ce yana da mutanen da yake da hulda da su a kasar ta Libya domin kaddamar da wannan yunkurin.

Sai dai kakakin gwamnatin Jamhuriyar Nijar din ya ce Saadi ya sabawa alkawarin da ya yiwa hukumomin na Nijar.

“Tun [watan] Agusta da suka zo nan”, in ji Malam Marou Amadou, “muka ce musu za mu yarda [mu ba su mafaka] ne idan ba za su jawo tashin hankali ba a Libya ko a wata kasa”.

Kakakin na gwamnatin Nijar ya kuma ce sun dauki mataki: “Mun dauki mataki—ba zai sake yin [irin wadannan maganganu ba], saboda mu ba ma son abin da zai sa tashin hankali ya shiga tsakanin Nijar da wata kasa”.