Sojojin Syria na cigaba da kai hari a Homs

Dan tawaye a Syria Hakkin mallakar hoto NA
Image caption Dan tawaye a Syria

Dakarun gwamnatin Syria sun sake kai sabbin hare haren bam a birnin Homs, a kwana na shidda a jere, a yunkurin da suke na murkushe 'yan tawaye.

Rahotanni sun ce, mutane 30 ne suka rasu a luguden wutar na yau.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon, ya ce yana fargabar abubuwan rashin imanin da ke faruwa a birnin na Homs, somin tabi ne na halin o-ni-'yasun da za a shiga a nan gaba.

Masu fafitika sun ce, dakarun gwamnatin Syriar na kara daukar matakai a kan iyakokin kasar da kasashen Jordan da Lebanon da Turkiya da Iraki, domin hana shigar da makamai a Syriar don 'yan tawaye.

Jamus ta kori wasu ma'aikatan ofishin jakadancin Syria su hudu, bayan an kama wasu mutane biyu da ake zargi da yin leken asiri a kan kungiyoyin adawan Syria da ke zaune a kasar ta Jamus.

Karin bayani