Kungiyar Al Shabaab ta hade da Al Qa'ida

Mayakan Al Shabaab Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mayakan Al Shabaab

Kungiyar nan mai tsats-tsauran ra'ayin Islama ta Al-Shabaab da ke Somalia ta bada sanarwar cewar ta shiga cikin Kungiyar Al-Qaeda.

An bayar da wannan sanarwar ce ta wani faifan bidiyo da shugabannin kungiyoyin biyu suka fitar.

Jagoran kungiyar Alqaedan, Aiman Al-zawahiri, ya yi lale marhabin da kungiyar Al Sabaab din.

Kungiyar Al Shabaab dai na da dubban mayaka, yawancinsu 'yan kasar Somalia.

Sai dai akwai wasu 'yan kasashen waje daga yankin da ma wasu wuraren daban.

Wasu da dama na ganin hadewar kungiyoyin zai sauya fadan da ake a Somalia.

Karin bayani