An sake kame Kabiru Sokoto

Harin Bom Acocin  Madalla Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A baya Kabiru Sokoto ya kufce daga hannun 'yan sanda bayan an kama shi

Kakakin gwamnatin Nigeria, Reuben Abati ya ce hukumomin kasar sun sake cafke mutumin nan mai suna Kabiru Sokoto, wanda ya kubuce daga hannun jami'an 'yan sanda a makonnin baya.

An ce an kame Kabiru Sokoto ne a wani kauye da ke Jihar Taraba.

Ana zargin Kabiru Sokoto da laifin kitsa harin nan na ranar Kirsimetin a wani coci da ke garin Madalla a Jihar Naija inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

Jami'ai a Najeriyar sun ce ya kubuce ne daga hannunsu bayan da suka ziyarci garin Abaji tare da shi domin gudanar da bincike.

Ko da yake har yanzu hukumomin tsaron Najeriyar ba su fito sun yi karin bayani kan kamun nasa ba, amma wasu majiyoyi da BBC ta yi magana da su a hukumar ta SSS sun tabbatar da cewa Kabiru Sokoton wanda bayanai ke nuna cewa babban jami'i ne a kungiyar Jama'atu Ahlussunah Lidda'awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram ya shiga hannun hukumar.

Shi ma kamfanin dillancin Labarai na Asociated Press ya ambato mai magana da yawun shugaban Najeriya Reuben Abati yana cewa, jami'an leken asirin kasar ne suka kama Kabiru Sakwaton a wani gari na jihar Taraba mai makwabtaka da jamhuriyar Kamaru.

Amma ya ce duk wani karin bayani sai a tuntubi hukumar leken asiri ta SSS.

Wata majiya a hukumar ta ce, an sake kame Kabiru Sokoton ne a garin Mutum Biu da ke jihar Taraba.

Jami'an tsaron Najeriya sun bayyana cewa, Kabiru Sokoto shi ne ya shirya makarkashiyar kai hari a kan cocin Katolika na St Theresa da ke Madalla, a ranar Kirsimetin da ya gabata, harin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.

Sai dai, Kabiru Sokoton ya tsere daga hannun jami'an 'yan sandan kasar kwana daya bayan kama shi, batun da ya zamanto babban abin kunya ga gwamnati da jami'an tsaron Najeriya.

Hakan dai ya janyo sauye-sauye a hukumar 'yan sandan kasar, inda Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya sallami Sifeto Janar din 'yan sanda na lokacin Hafiz Ringim tare da manyan mukarrabansa, sannan ya nada Muhammad Dahiru Abubakar a matsayin sabon Sifeto Janar.

Karin bayani