Ci rani na janyo cire yara a makaranta

Shugaban jamhuriyar Nijar, Muhamadou Issoufou Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban jamhuriyar Nijar, Muhamadou Issoufou

A Jamhuriyar Nijar iyaye mata dake zaune a yankunan karkara na ci gaba da kwarara zuwa birane domin ci rani.

Wannan lamari na tilastawa kananan yaran da iyayen kan tafi da su barin zuwa makaranta abinda kuma ke shafar makomar yaran.

Matsalar karancin abinci a kasar na taimakawa wajen kaurar da magidanta da ma iyaye matan ke yi da 'ya'yansu zuwa birane.