NEITI ta ce aikinta ba zai ci karo da kwamitin Ribadu ba

Hakkin mallakar hoto AP

A Najeriya hukumar dake binciken yadda ake kashe kudaden da ake samu daga ma'adanan man fetur na kasar, NIETI ta ce aikinta ba zai ci karo da kwamitin kula da harajin da kasar ke samu a bangaren man fetur ba, wanda aka nada Malam Nuhu Ribadu a matsayin shugaban kwamitin.

Hakan ya biyo bayan gazawar da wasu ke ganin hukumar ta yi da ya kaiga kafa kwamitin da tsohon shugaban hukumar yaki da yiwa tattalin arziki ta'annati ta EFCC, Malam Nuhu Ribadu, abinda hukumar ta NEITI ta musanta.

Tun bayan janye tallafin man fetur da gwamnatin Nigeria ta yi ne bayanai suka yi ta fitowa game da badakalar dake tattare da harkar man fetur ciki har da kudaden tallafi.