Zaben gwamna a jahar Bayelsa

Zabe a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zabe a Najeriya

A Najeriya, a yau ne aka gudanar da zaben gwamnan jahar Bayelsa - watau jahar da shugaba Goodluck Jonathan ya fito.

An shirya zaben ne bayan da a kwanakin baya kotu ta ce wa'adin mulkin wasu gwamnoni biyar, ciki har da na Bayelsar, ya kare tun kamar watanni bakwai a baya.

An ce an dauki tsauraran matakan tsaro a zaben na yau, kuma komi ya gudana lami lafiya.

'Yan takara kimanin 35 ne suka yi takarar a yau.

A yanzu haka an soma kidayar kuri'un.

Karin bayani