Za'a fara yajin aikin gama-gari a Masar

Masu bore a kasar Masar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu bore a kasar Masar

A yau ne masu fafutuka a kasar Masar za su fara yajin aikin gama-gari da kuma bijirewa don tursasawa gwamnatin mulkin soji gaggauta mika mulki ga farar hula.

Za'a fara yajin aikin ne a dai dai bukin cika shekara guda da murabus din da shugaba Hosni Mubarak yayi daga kan mulki bayan boren da aka yi a kasar.

Sai dai a wata sanarwa da ta fitar jiya juma'a, Majalisar sojin kasar ta zargi wadanda ta ce na kulla makarkashiyar neman ta da zaune tsaye a kasar.

Majalisar sojin ta kuma bayyana cewa sojojin kasar ba za su bada kai bori ya hau ba game da gaggauta mika mulki ga farar hula.