PDP ta lashe zaben gwamnan jahar Bayelsa

Zabe a Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zabe a Najeriya

Rahotanni daga jahar Bayelsa sun ce Hon. Henry Seriake Dickson, dan jam'iyyar PDP, shine ya lashe zaben gwamnan da aka gudanar a jiya.

An shirya zaben ne bayan da a kwanakin baya kotu ta ce wa'adin mulkin wasu gwamnoni biyar, ciki har da na Bayelsar, ya kare tun kamar watanni bakwai a baya.

'Yan takara kimanin talatin da biyar ne suka shiga zaben, wanda aka gudanar a cikin tsauraran matakan tsaro.

Karin bayani