Whitney Houston ta mutu

Whitney Houston Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Whitney Houston

Shahararriyar mawakiyar nan wacce kuma ta yi fina-finai 'yar kasar Amurka Whitney Houston ta mutu tana da shekaru arba'in da takwas.

'Yan sanda sun ce an samu gawarta ne a wani daki dake wani Otel a Beverly Hills, kuma kawo yanzu ba'a tantance musabbabin mutuwar ta ba.

Ita dai Whitney Houston ta yi wakoki dabam dabam da suka yi fice a shekarun 1980 da 1990 inda kuma ta samu kyaututtuka a matsayin mawakiya mace da ta fi kowa fice a wake-wake a duniya.

Mutuwar Whitney Houston ta yi matukar girgiza fannin wake-wake a Amurka da kuma masoya wakokinta a fadin duniya.