An kaddamar da sabbin kudi masu hoton Mandela

Sabbin takardun kudi da hoton Mandela Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sabbin takardun kudi da hoton Mandela

An kaddamar da wasu sabbin takardun kudi a kasar Afrika ta kudu dake dauke da hoton tsohon shugaban kasar, Nelson Mandela.

Shugaba Jacob Zuma ne ya kaddamar da kudin yau a pretoria, yayin bikin cika shekaru 22 da sako Mr Mandela, bayan ya shafe kusan shekaru talatin a kurkuku.

Shugaban Zuma ya bayyana cewa sako Mr Mandela da aka yi daga gidan yari ya bude wani sabon babi a tarihin kasar ta Afrika ta kudu.

Nan da 'yan watanni ne ake fatan fara amfani da sabbin takardun kudin a kasar.