An hallaka mutane a Zonkuwa da Maiduguri

Tsaro a Maiduguri
Image caption Tsaro a Maiduguri

Wasu mutanen da ba'a san ko su wanene ba sun kai hari cikin daren jiya a garin Zonkuwa dake kudancin jihar Kaduna a Najeriya.

Bayanan dake fitowa daga garin na nuna cewa akalla mutane biyu sun hallaka a sanadiyyar harin, yayin da wani mutum kuma ya sami raunuka.

Rahotanni sun ce, a daren jiya ne wasu mutane dauke da muggan makamai suka kai harin a Unguwar Musa da ke garin na Zonkwa.

Rundunar 'yan sandan jahar na cigaba da neman wadanda suka yi aika-aikar.

Tun bayan zaben bara ne dai ake samun tashe tashen hankula a kudancin Kadunar.

A jahar Borno ma, mazauna tsohon garin Maiduguri da ke karamar hukumar Jere sun wayi gari cikin firgici, sakamakon kisan wulakancin da aka yi wa wasu mutane ukku, ta hanyar yanka su.

Kazalika rahotanni sun ce an kuma harbe wasu mutane biyu har lahira.

A makon da ya gabata ma an yi irin wannan kisan wulakanci ga wasu mutane 6 a birnin Maiduguri.