Girka ta amince da matakan tsuke bakin aljihu

Firai ministan Girka, Lucas Papademos Hakkin mallakar hoto NA
Image caption Firai ministan Girka, Lucas Papademos

Majalisar dokokin kasar Girka ta amince da wasu matakan tsuke bakin aljihu masu tsauri a matsayin kandagarki ga durkushewar tattalin arzikin kasar da kuma ci gaban kasancewarta a kungiyar kasashen masu amfani da kudin Euro.

Hakan na daga cikin sharudda uku da kungiyar tarayyar turai da kuma Hukumar bada Lamuni ta Duniya IMF suka bukaci kasar Girka ta cika, kafin a amince a bata karin kudin na Euro biliyan dari da talatin don ceto tattalin arzikin kasar.

Kashi biyu bisa uku na 'yan Majalisar ne suka kada kuri'ar amincewa da matakin tsuke bakin aljihun, yayin da kuma da dama daga 'yan majalisar da suka nuna rashin amincewa aka kore su daga gamayyar jam'iyun dake mulki.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da dubban 'yan kasar ke bore game da matakin a gaban harabar majalisar, inda suka cinnawa wasu gine-gine wuta.