Kotu ta tuhumi Firai ministan Pakistan

Firai ministan Pakistan, Yousuf Raza Gilani Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Firai ministan Pakistan, Yousuf Raza Gilani

Kotun kolin kasar Pakistan ta tuhumi Firai ministan kasar Yousuf Raza Gilani da laifin 'kin bin umurnin kotu.

Mista Gilani ya musanta cewa ya aikata wannan laifi inda kuma aka dage sauraron shari'ar har zuwa nan gaba cikin wannan watan.

Ana dai zargin shi ne da kasa sake bude shari'ar zargin aikata cin hanci da rashawa akan shugaba Asif Ali Zardari.

Idan aka same shi da laifi, zai fuskanci daurin watanni shida kuma za'a haramta masa ci gaba da kasancewa a kan mukaminsa.

Ana zargin shugaba Zardari ne da amfani da asusun ajiya a wasu bankuna dake kasar Switzerland wajen karkata kudaden da yake karba a matsayin cin hanci, zargin da ya musanta.