Kungiyoyi na yunkurin samar da zaman lafiya a Plato

'yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'yan sandan Najeriya

Kungiyar direbobin motocin haya sun fara yunkurin samar da zaman lafiya a jihar Pilato dake arewacin kasar.

Kungiyar ta gayyaci masu ruwa da tsaki, inda aka bada kasidu akan muhimmancin dorewar zaman lafiya a jihar.

Jihar Filato dai ta dade tana fama da ringingmu masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa, sun gurgunta harkokin kasuwanci da ci gaban jihar.

Masana dai na ganin sai hukumomi sun kara hobbasa, kuma jama'a sun taimaka wajen dorewar tsaro a jihar.