An dau matakan hana zanga-zanga a Bahrain

Masu zanga zanga a Bahrain Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga zanga a Bahrain

Hukumomi a Bahrain sun rufe cibiyar hada-hadar kudi dake birnin Manama, kana kuma suka rufe babbar hanyar mota dake zuwa yammacin babban birnin, yayin da 'yan Shi'a dake adawa da masarautar kasar ta mabiya Sunni, ke tuna cika shekara guda da yunkurin kawo sauyi irin na dimukradiyya a kasar.

'Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zanga dake jifa da duwatsu.

Wakilin BBC yace mabiya Sunni ne dai ke mulkin kasar ta Bahrain, kuma masarautar Sarki Hamad bin Isa Al Khalifa tace, tana cika alkawuran da tayi na kawo sauyi ta fuskar siyasa a kasar da kuma daukar mataki akan yadda 'yan sandan kasar ke aikinsu.

Karin bayani