Hukumomi a Burtaniya sun ba da belin Abu Qatada

Abu Qatada Hakkin mallakar hoto AP
Image caption An ba da belin Abu Qatada a Burtaniya

Hukumomin Burtaniya sun ba da belin malamin nan mai tsananin kishin Islama wato Abu Qatada wanda jami'an Burtaniyan ke zargin yana daya daga cikin manyan Shugabannin Kungiyar Alqaeda.

Ana tsare da Abu Qatada ne a gidan Yarin Burtaniyan tun fiye da shekaru shida da suka gabata a lokacin da ake ta kokarin ganin an mika shi ga hukumomin Kasar sa Jordan, wurin da za a caje shi da laifuka na ayyukan ta'addanci.

To amma Kotun kare hakkin 'yan adam ta Tarayyar Turai ta hana a mika shi ga hukumomin na Jordan, saboda fargabar cewa ba za a yi masa shari'ar adalci a can ba.

Gwamnatin Burtaniyan dai ta ce Abu Qatada yana barazana ga tsaron kasa, amma babbar Kotun Kasar ta nemi a bayar da belin sa bisa tsauraran sharudda.

Karin bayani