Bam ya kashe dan sanda a Kaduna

kaduna
Image caption Dan sandan da ya yi kokarin kwance bam din ya rasa ransa

Wasu bama bamai biyu sun fashe a Unguwar Sarki dake tsakiyar jihar Kaduna, inda bayanai suka nuna cewa ya hallaka jami'in tsaro daya sannan ya tawarwatsa wata motar sufuri.

Wakilin BBC a Kaduna, Nurah Muhammed Ringim yace yaga gawar dan sanda wanda ya rasa ransa a kokarin kwance daya daga cikin bam din da aka dasa.

A safiyar ranar Talata ne, lamarin ya auku a garin Kadunan inda bam biyu suka fashe.

Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai wannan harin amma kuma jami'an tsaro sun ce sun gano wasu karin bama baman da basu fashe ba.

Wannan lamarin ya faru ne kwana guda bayan da sojoji a kofar shiga fadar gwamnatin jihar Kaduna suka harbi wani jami'in gwamnati bayan da yayi kokarin kutsawa cikin gidan gwamnan ta kofar da bai kamata yabi ba.

Rahotanni daga Maiduguri sun ce, an kona wani kantin saida magani a hanyar kasuwar shanu da ke unguwar Gamboru Ward.

Shaidu sun ce an sami asarar rayuka.

A cewar rundunar tabbatar da tsaro ta hadin gwiwa a Maidugurin, wani mutum ne ya je sata a kantin sayar da maganin, ya kashe mutum guda kamin daga baya ya cinnawa kantin wuta.

Karin bayani