'Talauci ne ke haifar da rikici a yankin Sahel'

Mali
Image caption Masana sun ce babu tsaro sosai a yankin na Sahel

Shugaban Nijar Muhammadu Isoufu ya bayyana yakin da aka yi a kasar Libya da talauci daga cikin dalilan da suka haifar da rikicin da ake fama da shi a yanzu tsakanin gwamnatin kasar Mali da 'yan tawayen Abzinawa da ke son kafa kasar Azawad.

Shugaban na Nijar ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da ya yi da wata jaridar kasar Faransa Le Monde.

Shugaba Isoufou ya kuma tabo batutuwan da suka shafi barazanar yunwa da ke fuskantar Nijar, da yadda hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa a makwafciyar kasar Najeriya ke barazana ga kasarsa da ma batun kasancewar sojojin kasar Faransa a jamhuriyar Nijar.

Shugaba Muhammadu Isuhu ya ce: "muna da masaniyar cewa an sace makamai da dama a lokacin yakin Libya, makaman da aka karkatar da su zuwa kasashen Nijar, Mauritaniya, Chadi da sauransu.

Makaman da a yanzu dakarun da suka mara baya ga marigayi shugaban kasar Libya Muammar Ghaddafi ke amfani da su wajen yakar gwamnatin kasar Mali", a cewar Muhammadu Isoufu.

Shugaban ya kara da cewa kasashen Sahel musamman Nijar da Mali suna da tarihin fama da tawaye a shekarun 1990, sai da yakin kasar Libya a yanzu ya karfafi 'yan aware a Mali wadanda suke son kafa kasar Azawad.

Kwararar 'yan gudun hijira

Dangane da tasirin da yakin da ake yi a kasar ta Mali ke yi a kasarsa Nijar kuwa, Shugaba Muhammadu Isuhu ya ce tuni Nijar ta karbi bakuncin 'yan gudun hijira dubu goma da suka hadar da sojoji, kuma idan yakin ya ci gaba, akwai yiwuwar wasu dubban su tsallaka iyaka zuwa Nijar din.

Kuma dama tuni Nijar din take fama da dubun-dubatar 'yan kasarta da suka koma gida sakamakon rikice-rikicen kasashen Libya da Ivory Coast.

"Hakan ya sa muna kara kashe kudade a kan harkokin tsaro da na soji". A don haka in ji shi: "Rikicin kasar ta Mali na ci wa Nijar tuwo a kwarya".

Dangane da batun ko Abzinawan Nijar ka iya kwaikwayon takwarorinsu na Mali kuwa, shugaba Isuhu ya ce hakan na iya yiwuwa.

Sai dai sun shirya taron zaman lafiya a yankin Sahel a kwanakin baya, wanda ya samu halartar tsaffin shugabanin 'yan tawayen Nijar, kuma gwamnatinsa na kokarin yraya yankunan makiyayaya inda ake samun Abzinawa da dama.

'Mun damu da rikicin Boko Haram'

Da aka tambaye shi ko zai dogara da Faransa domin kare kasarsa daga irin abinda yake faruwa a Mali, sai shugaba Isuhu ya ce babu kasar da za ta dogara da wata kasar domin kare mata kasar ta.

Ya kuma musanta cewa akwai sojin Faransa a Nijar da suke horar da dakaru na musamman.

Dangane da hare-haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa a Najeriya kuwa, shugaba Isufou Muhammadu ya ce Nijar ta damu da abinda ke faruwa a makociyar tata.

Amma ya yi amannar gwamnatin Najeriya za ta iya shawo kan lamarin.

Sai dai ya tabbatar da cewa akwai alamun da ke nuna cewa akwai alaka tsakanin Boko Haram da Alshabab ta Somaliya, amma suna kokarin cewa hakan bai tabbata ba.

Ya kuma kara da cewa, gwamnatinsa na kokari wajen ganin ta shawo kan matsalar yunwar da ke barazana ga kasar.

Karin bayani