Kyautata alaka tsakanin Amurka da China

Kyautata alaka tsakanin Amurka da China
Image caption China da Amurka na fama da bambamce-bambamce ta fuskar kasuwanci da musayar kudi

Shugaban Amurka Barack Obama ya kalubalanci shugaban kasar China mai-jiran-gado kan harkokin kasuwanci da kuma kare hakkin bil'adama.

Da yake ganawa da mataimakin shugaban kasar China Xi Jinping a fadar White House, Mr Obama ya ce yana da muhimmanci Amurka ta ci gaba da huldar kut-da-kut da China.

Mr Xi ya ce yana fatan ziyarar ta sa za ta karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu masu karfin fada aji.

Amurka da China na fama da bambamce-bambamce ta fuskar kasuwanci da musayar kudi da kuma kare hakkin bil'adama.

Mr Xi, dan shekaru 58, shi ne ake sa ran zai gaji shugaban China Hu Jintao, wanda wajibi ne ya yi ritaya daga shugabancin jam'iyyar Kwamunisanci a bana, sannan ya bar shugabanci a shekara ta 2013.

'Muhimman abubuwa'

Amurka ta dade tana matsa lamba ga Beijing kan abinda ta kira rashin adalci a harkokin kasuwanci, da darajar kudadenta da kuma satar fasaha.

"Muna bukatar yin aiki tare da China domin tabbatar da cewa kowa na aiki kan ka'idojin kasuwancin da aka amince da su," a cewar Mr Obama, wanda ke tare da Mr Xi.

"Wannan ya hada da tabbatar da cewa akwai daidaito kan harkokin cinikayya bawai kawai tsakanin Amurka da China ba, harma da sauran sassan duniya."

Ziyarar Mr Xi na zuwa ne a daidain lokacin da ake nuna damuwa kan yadda China ke murkushe masu zanga-zangar neman 'yancin Tibet.

Masu kare hakkin bil'adama sun gudanar da zanga-zanga a wajen fadar White House a lokacin da mataimakin shugaban Chinar ya isa fadar.

Ana sa ran Mr Xi zai ziyarci wata gona a Iowa ranar Alhamis kafin ya tashi zuwa biranen Los Angeles da California, domin ganawa da shugabannin 'yan kasuwa a can.

Karin bayani