An haramta bukin 'Valentine' a Uzbekistan

uzbekistan Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasu masoya a kasar Uzbekistan

Masoya a kasar Uzbekistan wadanda suke bukin ranar masoya wato 'Valentine' ta hanyar sauraron wakokin Rayhan, a bana sai dai su nemi wata hanyar nishadantar da kansu.

Rayhan shahararren mawaki wanda salon wakarsa ya hada da irin na gargajiya da kuma na Turai, ya shafe shekaru yana wakoki a duk ranar 14 ga watan Fabarairu.

Amma a bana, an dakatar da bukin na wakokin tare da sauran wasu abubuwan nishadin.

A maimakon bukin ranar masoya ko kuma Valentine, hukumomi a kasar na kokarin jawo hankalin 'yan kasar don su jinjinawa wani attajirin sarkin kasar mai suna Babur, wanda shima ranar haihuwarsa take 14 ga watan Fabarairu.

Babur wanda jikan Genghis Khan ne wato wanda ya kirkiro al'adu da juriya a tsakanin Kudanci da tsakiyar nahiyar Asiya, za a tuna dashi ta hanyar yin karatun littatafai da kuma na adabi.

Wani jami'i a sashin wayarda kan jama'a da kuma bunkasa al'ada na ma'aikatar ilimin kasar ya ce akwai dokar data haramta yin bukukuwa da suka sabawa al'adun kasa, a don haka sai dai ayi bukin ranar haihuwar Babur.

Jami'in wanda bai yadda a ambaci sunansa ba, ya ce dokar ta dade tana aiki.

Jama'ar Uzbekistan sun rarrabu akan wannan matakin, wanda shi ne lamari na baya bayannan dake nuna adawa akan tsarin yammacin duniya.

Abdullaw wani mazaunin Tashkent wanda ya bayyana kansa a matsayin kwararre, ya ce matakin gwamnati na hana bukin Valentine ya yi dai dai.

Yace "Zagayowar ranar haihuwar babban shugabanmu Mohammed Zahiriddin Babu, to me yasa zamu yi bukin wani abu na kyalkyali daya sabawa tarihinmu".

Amma Jasur Hamraev, wani dan jarida ya ce tilastawa mutane kishin kasa ba daidai bane.

Hamraev yace "bai kamata rana kamar wannan a maida ta abun kishin kasa saboda hakan raba kan al'umma ne saboda matasa sun so ace sun je kallon wakokin Rayhan".

Rahotanni sun nuna cewar ma'aikatar labarun kasar a baya ta yi gargadin masu wallafa jaridu su daina wallafa abubuwa da suka shafi ranar 'Valentine' .

Amma wata dalibar jami'a ta shaidawa BBC cewar ranar masoya ta kasance wata sabuwar al'ada a tsakanin matasa inda suke musayar katunan fatan alheri ga masoyansu.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Diyar shugaban Uzbekistan Karimova

Shafin intanet na uznew.net na kasar ta Uzbekistan ya gudanar da nashi kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a akan batun bukin, kuma yawancin jama'a sun ce zasu fita da masoyansu su ci abinci kuma su je kulob.

Daya daga dalibai a kasar ya ce "abun kunya ne a maimakon zuwa wajen waka zamu bata lokaci akan adabi a cikin jami'a.

Ba dai wannan ne karon farko da hukumomi a kasar da kafar yada labaru mallakar gwamnati suka bullo da shirin kawar da al'adun yammacin duniya ba.

A makwanni da suka wuce an buga kasidu ana sukar finafinan kasashen waje daga Mexico da kuma yankin Latin Amurka saboda suna bata al'adun gargajiya.

Ana matukar sukar wakoki inda aka bayyanasu a matsayin ayyukan shedan masu koyarda shaye-shaye da kuma abubuwa na badala.

Gwamnati ta kafa wani kwamitin tacewa da kuma sa'ido akan wakoki da kuma mawaka saboda kaucewa amfani da baitocin batsa.

Masu lura sun ce matakin hukuma akan sukar al'adun yammacin duniya da kuma tace abubuwa a talabijin da intanet ya zama kamar baki biyu, saboda gwamnati bata yin komai akan irin wakokin 'yar shugaban kasar Gulnara Karimova.