An kai hare hare a jahar Borno

Hari a Najeriya
Image caption Hari a Najeriya

Rahotanni daga jihar Borno sun ce, da yammacin yau wasu 'yan bindiga sun sake kai hare hare a unguwar Gamboru da ke tsakiyar birnin Maiduguri, inda suka harbe wani mai shagon aski har lahira, suka kuma jefa gurneti tare da harbin kan mai tsotsayi.

Rahotannin kuma sun ce, an samu asarar rayuka da dama a kauyen Duguri da ke arewacin jihar Bornon, bayan da wasu da ba a san ko su wanne ba suka cinna wa kauyen wuta da tsakar daren jiya.

Hakan na zuwa kwanaki biyu bayan hallaka wasu mutane bakwai da wasu 'yan bindiga suka yi a kauyen.

Rundunar Hadin Gwiwar Samar da Tsaron Maidugurin ta tabbatar da abkuwar lamarin.

Hukumar tsaron Najeriyar ta farin kaya SSS, ta wallafa hoton wani mutum wanda ta ce yana amfani da sunayen Habibu Bama ko Shuaibu Bama ko Habib Mamman, wanda take nema ruwa a jallo, bisa zarginsa da hannu wurin tada bam din Madalla na ranar Kirismeti da ta wuce.

A cewar hukumar ta SSS, mutumin tsohon soja ne, harshensa na asali Kanuri, kuma ya fito ne daga garin Bama na jihar Borno.

Karin bayani