Gwamnatin Kano ta tallafawa wadanda harin Boko Haram ya shafa

Wadanda hare-haren Boko Haram su ka shafa
Image caption Gwamnatin Kano ta soma tallafawa iyalan wadanda hare- haren Boko Haram su ka shafa

Gwamantin jihar Kano a arewcin Najeriya ta bada tallafi ga iyalan wadanda hare- haren watan jiya ya hallaka a jihar, inda ko wane iyali ya samu Naira Miliyan Daya.

Gwamnatin dai tace ta bada tallafin ne wanda tace somi tabi ne daga cikin sama da Naira miliyan 200 da ta karba daga hukumomi, da gwamnatoci da kuma daidaikun mutane.

Gwamnan Jahar Kano Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso ya shaidawa BBC cewar gwamnatin Kanon za ta cigaba da aikin tantance mutanen da hare-haren Kungiyar Boko Haram ya shafa, domin ba su irin wannan tallafi.

Haka kuma gamayyar masu fada aji a jihar sun sake taruwa, inda kwamitin mutane 15 da aka kafa dan bada shawarar yadda za'a inganta al'amuran tsaro yayi bitar rahoton da ya mikawa gwamnati.

Karin bayani