Rayuwa za ta tabarbare a yankin hamada na Afirka

Taswirar Afirka
Image caption Rayuwa za ta tabarbare a yankin hamada na Afirka sakamakon rashin kyawun damuna

Hukumomin ba da agaji na Majalisar dinkin duniya sun yi kashedin cewa sha'anin rayuwa zai yi mummunar tabarbarewa a yankin hamada na Afirka saboda rashin kyawun damuna a Kasashe da dama.

Yayin da suke jawabi a birnin Geneva, jami'an ayyukan agajin sun ce mutane miliyan ashirin da uku na fuskantar hadarin karancin abinci a Kasashen Niger da Chadi, da Mali da Mauritania, da Burkina Faso da kuma Senegal.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta yi gargadin cewa, lamarin zai iya zama wani babban bala'i muddin dai Kasashen duniya masu bayar da agaji ba.

Karin bayani