Sarkozy zai sake takarar shugabancin Faransa

Shugaban Faransa, Nicolas Sarkozy, ya tabbatar da cewa zai nemi wa'adin mulki na biyu a zaben da za'a yi a watan Aprilu dake tafe.

Shugaba Sarkozy ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi ta talabijin.

Yanzu haka dai Mista Sarkozy yana bayan babban abokin karawarsa na jam'iyyar gurguzu, wato Francois Hollande, a kuri'ar jin ra'ayin jama'a.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Nicolas Sarkozy

Masu lura da al'amura dai sun ce, saboda hakan Mista Sarkozy na da jan aiki a gabansa a yakin neman zabe.

Karin bayani