Ana taro domin sasantawa da 'yan Taliban

Shugaban Afghanistan da Praministan Pakistan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Afghanistan da Praministan Pakistan

Shugaban kasar Afghanistan Hamid Karzai yace gwamnatinsa ta tattauna ta bangarori uku tare da Amurka da kuma kungiyar Taliban.

Wakilin BBC a Kabul yace wanan shine karon farko da shugaban kasar ya amince cewa akwai tattaunawar dake gudana tsakaninsu.

Mr Karzai ya sanar da haka ne a wata hira da ya yi da jaridar Wall street gabanin ziyarar da zai kai kasar Pakistan.

Yanzu haka dai Shugaba Karzai na kasar Pakistan domin halartar taron tattaunawar kwanaki uku da mahukuntan kasar Pakistan a Islamabad.

Jim kadan bayan isar sa Pakistan din shugaba Karzai ya gana da firaminisata Yousouf Raza Gilani,da kuma Ministan harkokin wajen Iran Ali Akbar Salehi wanda shima zai halarci taron kasashen uku.

Karin bayani