Pursunoni sun tsere a wani gidan yari a Kogi

Gidan yari a Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gidan yari a Najeriya

Harin da aka kaiwa wani gidan yari a Nigeria ya sa fursononi kusan dari biyu sun tsere.

Wani jamian gidan yarin ya hallaka a lokacin da 'yan bindiga sukayi amfani da karfi wurin bude kofofin gidan yarin, a wani gari dake kudu da birnin Abuja.

Mutum daya kacal aka bari a gidan yarin. Sai dai Wata Jamiar hulda da jama'a ta hukumar gidan yari ta Nigeriayar ta musanta zargin da ake akancewa ' yan kungiyar boko haram ne keda alhakin kai harin.

Sai dai bata yi karin haske akan dalilin da yasa tace basu bane.

A watan Satumba ta shekerara 2010 'yayan kungiyar boko haram su kayi nasara wurin taimakawa fursononin dari bakwai tserewa a wani hari makamanci haka.

Karin bayani